Hukumar dake kula da kare hakkin mutane a jihar Neja ta tasa keyar wani magidanci da ta kama ya banka ma dan sa mai suna Bello Musa wuta.
Kamar yadda shugaban hukumar Maryam Kolo ta sanar wa kamfanin dillanci labarai, ta ce mahaifin Musa ya daure shi inda daga nan ya dildilo fetir daga babur din sa sannan yako kwara wa yaron, ya kyasta ashana abin sa a jikin yaro.
Nan take kuwa yaron ya fara ihu yana kira a cece shi. Kafin ya babbake makwabta suka kawo masa dauki.
Da yake amsa laifin sa, Musa yace yayi haka ne ganin yadda shi Bello ya addabi babban wansa da fitina.
Ya ce a yafe masa cewa fushi ne yayi lokacin.
Yanzu dai Bello na asibitin Umaru Ndayako dake garin Minna a kwance.