Menene doka ta ce game da likita ya bude asibitin kansa bayan yana wa gwamnati aiki

0

Mafi yawan lokuta mutanen Najeriya na kokawa da yadda wasu likitocin dake aiki a asibitocin gwamnati ke aika marasa lafiya asibitoci mallakan su mai makon basu kula a inda suke aiki.

Hakan dai ya kan hana likitocin mai da hankali a aikin su a asibitocin gwamnati da suke aiki.

Duk da cewa akwai doka da ta ba likitoci da likitocin hakora daman iya duba mutane domin samun dan kudade bayan sun kammala aikin su a asibitocin gwamnati da kuma lokutan da suke hutu. hakan dai wasu

A hiran da gidan jaridar ta wani ma’aikacin hukumar MDCN ta gano cewa hakan da likitocin ke yi ba daidai bane kuma suna aikata haka ne saboda dama da suka samu na wata doka da aka yi a zamanin mulkin Ibrahim Babangida wanda ya yarda wa likita da ke aikin gwamnati ya bude tasa asibitin sai dai ban da kwantar da mara lafiya.

Dalilin haka ne ya sa wasu likitocin suke bude nasu asibitin sannan su yi watsi da na gwamnati inda ya kamata ace nan ne suka mai da hankulan su.

Likitan ya ce an yi gyara ga wannan doka inda ya hana duk likitan dake aiki a asibitin gwamnati bude nasa asibitin.

‘‘Dokar ta baiwa likitocin da ke aiki a asibitin gwamnati ikon mallakar gona ne kawai.”

Amma duk da hakan wasu likitocin basu daina ba wanda hakan ya sa ministan kiwon lafiya sanar da cewa daga ranar 11 Okotoba gwamnatin za ta gyara dokar domin yi wa likitocin iyaka a aikin su da wanda za su iya yi.

Isaac Adewole yace hakan da zai taimaka wajen wayar da kan mutane da likitoci sanin hakokin su da yadda zasu iya kare su.

Share.

game da Author