Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koka da yadda manyan yankin kudu maso gabas suka nuna halin baruwan mu da yadda wasu tsagerun matasa a yankin suke kokarin maida da hannun agogo baya ta hanyar tado fitina a kasarnan.
Buhari ya fadi haka ne a jawabinsa na Cikan Najeriya shekara 57 da samun ‘yancin Kai.
“Ina karamin soja da ni aka yi yakin basasa har aka gama ina ciki tsundum. Yakin nan ya haifar da asarar rayuka kusan milyan biyu. Ya kuma kawo asarar dukiyoyi da halin kunci matuka.
“Wadanda ke ta hauragiya da tayar da jijiyar wuyar maimaita Yakin Basasa a kasar nan, ba a haife su kafin 1967 ba. Kuma ba su da masaniyar balbalin-bala’in illar basasar da mu ka shiga.
“Girman wasu manyan wancan yanki ya zube a ido na, ganin yadda su ka kauda kai daga yi wa matasan su ‘yan zafin kai kakkausan gargadi da shaida musu bakar wahalar da Yakin Basasa ya haddasa.
“Ya kamata wanda ya dandani zafin Yakin Basasa su sanar wa wadanda ba a haifa a lokacin ba, cewa sake tayar da batun basasa wauta ce, ba karama ba.
Discussion about this post