Masu tsoma ni cikin harkallar Maina rudaddu ne – Inji Jonathan

0

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa duk wani mai kokarin tsoma shi ko danganta shi da rikicin harkallar kudin fansho, to rudadde ne.

Ya kara da cewa borin kunyar da wasu ke yi da nufin danganta shi da laifin dawo da Maina a cikin kasar nan a asirce, ya nuna irin tosasshiyar kwakwalwa da wasu a cikin gwamnatin Buhari ke da shi.

‘‘Saboda akalar gudanar da mulki ta subuce musu har sun kauce hanya, sun fara hauragiya wai Shugaba Jonathan ne ya dawo da Maina har ya kara masa mataki biyu a cikin 2013.’ Haka kakakin Jonathan Ikechukwu ze ya shaida wa PREMIUM TIMES.

‘Yakamata gafalallun mutanen nan su daina daukar mutane shashashu. Ya ci gaba da cewa ya kamata su daina borin-kunya su fito su fada wa ‘yan Najeriya gaskiya cewa laifi dai sun yi shi kawai.

Gwamnatin Buhari ta sha suka da caccaka tun bayan da PREMIUM TIMES ta fallasa cewa an dawo da Maina bakin aikin sa a asirce.

Manyan ministocin Buhari na harkokin cikin gida da na shari’a har ma shugabar ma’aikata sun ta dora wa juna laifin dawo da Maina, har abin ya kai ga alakan ta shi da Jonathan.

Share.

game da Author