Majalisar Tarayya ta yi bikin tsige Babachir Lawal

0

Majalisar Tarayya ta bayyana cewa korar Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya wanke su kuma ya gaskata binciken da su ka fara yi a kan harkallar sa ta kwangilar datse ciyawa a kogin Yobe da wasu kwangiloli a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Daga nan sai majalisar ta umarci sauran kwamitocin da aka dora wa nauyin binciken sauran harkalla a cikin kasar nan da su gaggauta kammalawa tare da gabatar da rahotannin su domin a dauki matakan da su ka dace.

Wannan matsaya da majalisar ta dauka, ta biyo bayan wani roko ne da Sanata Bala Na’Allah ya gabatar a yau Talata.

Na’Allah ya kara da cewa kokarin da wasu ‘yan bulkara su ka yi domin su bata sunan Majalisar Tarayya, bai yi nasara ba.

Share.

game da Author