Majalisar Barno ta dakatar da zama saboda sharara ma wani dan majalisar Mari da Sanata Ndume yayi

0

Kakakin majalisar dokokin jihar Barno Abdulkareem Lawal, ya dage zaman majalsar cewa ba za ta sake zama ba sai an bi ma wani dan majalisar jihar mai suna Bukar Daja-Ali da sanata Ali Ndume ya sharara wa mari a wani taro da akayi a jihar.

Majalisar ta ce ba za ci gaba da zama ba har sai an bi ma dan majlisan hakkin sa.

Ta rubuta wa Sufeton janar din ‘yan sandan Najeriya domin daukan mataki akai.

Bayan haka Kuma Majalisar ta yi kira ga rundunar ‘yan sandan jihar da su binciki hari da aka kai wa wani dan majalisar dake wakiltan Kwaya Kusar da wasu matasa suka kai masa.

Sanata Ali Ndume ya karyata hakan inda ya musanta wannan zargi da majalisar jihar ta ke yi a kansa.

Share.

game da Author