Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa maida Abdulrasheed Maina a kan aikin sa ya kara tabbatar da cewa “akwai garken barayin da APC ke kallo da martaba.’
Jam’iyyar ta kara da cewa tunda har gwamnatin APC za ta sake dawo da wanda ake zargi da danne biliyoyin kudin fansho, kuma har ya gudu ake neman sa, amma aka dawo da shi a asirce, hakan na kara tabbatar da irin tukin gangancin da ake yi wa kasar nan da sunan mulki.
Sakataren Yada Labaran PDP, Bayo Adeyeye ya kara da cewa PDP ba ta gamsu da korar Maina daga aiki ba, wanda Shugaba Buhari ya bada umarnin gaggautawa a yi.
” Ahaf! To don Buhari ya ce a gaggauta korar Maina sai me? Ai Abokin damo, to guza ne. Idan ba haka ba, ta yaya jam’iyya mai mulki za ta dawo da wanda ake nema ruwa a jallo, kuma a ba shi mukami a asirce?
“Duk mutumin kirki mai mutunci ba zai manta da yadda gwamnatin mu ta PDP a wancan lokacin ta bai wa Maina mukami ba.
Amma sai ya jefa kan sa cikin harkallar naira biliyan 100, kuma ya tsere lokacin da EFCC ke neman sa.”
A karshe PDP ta yi kakkausan gargadin cewa a gaggauta cire Maina kuma a kore shi daga aiki, tare da cafke shi, a hukunta shi tare da duk masu hannu wajen maida shi aiki a asirce.
MAINA YA SHIGA WASAN BUYA DA EFCC
Wata sabuwa wai inji ‘yan caca. A daidai lokacin da ake rubuta wannan labari, sahihan bayanai sun tabbatar da cewa Maina ya boye, tun bayan da ya samu labarin cewa EFCC sun fara farautar sa a baya-bayan nan.
Farautar Maina ta zo ne bayan sanarwar da ta fito daga Fadar Shugaban Kasa inda ya bayar da umarnin a gaggauta korar Maina daga aiki.
Discussion about this post