Iyalan tsohon shugaban kwamitin tara kudaden fansho, Abdulrashid Maina, sun fito a ranar Laraba su na kare dan uwan su, tare da ikirarin cewa a daina kiran Maina macuci ko mazambaci. Maimakon haka, sun bayyana cewa Maina maceci ne ba macuci ba.
Yayin da su ke wa manema labarai jawabi a Kaduna, Aliyu Maina ya ce dan’uwan su ya shiga kwamitim da kyakkywar aniyar tsarkake harkallar da aka rika yi a harkar fansho, kuma ya yi kyakkyawan aikin da yi.
Don haka ya ce Maina bai aikata wani laifi ba, kawai dai garken wasu kuraye ne wadanda ya hana yin watanda da bilyoyin kudade su ke neman a yanzu su ga bayan sa.
Ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya taimaka wajen dawo da Maina domin ya taimaka wajen yaki da ake yi wajen kawo ingantaccen canji a kasar nan.
Ya kuma ce iyalan Maina su na rike da kwafen takardun da suka tabbatar da cewa garken kuraye ne su ka tasa Maina a gaba domin su bata masa suna, saboda sun san shi idan maganar harkalla ce, su ne ’yan harkalla, amma Maina tsarkakke ke.
“Saboda bakin jini sa kuma kashin kajin da su ke son tilas sai sun goga wa Maina, har fa wadannan garken kuraye sun je gidajen Maina sun shafa masa jan fenti, da sunan ‘EFCC.’
‘‘Maina ya yi wa kasar nan aiki, ya hana garken kuraye su kwashe biliyoyin kudi a asusun fansho na ma’aikatan gwamnati da kuma asusun fanshon ‘yan sanda.”