Wata kungiyar masoya shugaban Kasa Muhammadu Buhari za suyi zanga-zanga gobe Laraba domin nuna goyon bayan su ga Buhari ranar Laraba a Abuja.
Bayan haka kuma za su yi amfani da wannan zanga-zanga don kira ga shugaban kasa ya tsige shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.
Wannan gangami da tattaki za a farashi da karfe 6 na safe ne zuwa 6 na yamma. Kuma zai taso daga wurin hutawa na ‘Unity Fountain’ ne dake garin Abuja.
Kamar yadda jaridar Saharareporters ta ruwaito, kungiyar na kira ga duk yan Najeriya da su halarci wannan zanga-zanga.
“ Muna kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su fito kwansu da kwarkwata su halarci wannan zanga-zanga domin nuna wa shugaban kasar mu goyon baya da muke masa da kuma gode wa Allah zabin da yayi mana shi, mutum mai gaskiya domin ya ceto kasar mu Najeriya.”
“ Bayan haka kuma za mu yi amfani da hakan domin domin kira ga shugaban kasa da ya kori shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, wato Abba Kyari, saboda rashin kirkinsa da amfani da ofishin sa domin yin abin da ya ga dama a wannan gwamnati.”
Kungiyar ta kara da cewa Abba Kyari, yana amfani da kujerar sa don cin Karen sa babu babbaka, wanda hakan ya sa ana samun tafiyar hawainiya a aiyukan gwamnati. Hakan ya na faruwa ne dalilin hana shugaban kasa ganawa da ministoci, gwamnoni da wasu ‘yan Najeriya a lokacin da ya kamata.
Discussion about this post