Dubban yan Kungiyar yan uwa musulmai ne suka gudanar da tattaki a garin Zariya, jihar Kaduna.
Mabiya kungiyar da ya hada da matansu sun rarrabu ne a titunan Zariya domin gudanar da tattakin.
Wannan tattaki dai suna yin shine suna cewa Lababaika Ya Hussein.
Kamar yadda wasu daga cikin wadanda suka halarci tattakin, komai an yi cikin kwanciyar hankali babu tsangwama ko tarereniya.
Wani dan kungiyar Muttaqa Kumasi, da ya saka hotunan a shafinsa na Facebook ya kara da cewa, Sheikh Abdulhamid Bello shine ya jagoranci wacce aka dauko daga Kofar Kuyan Bana.
Discussion about this post