Likitocin Asibitocin gwamnati a jihar Kaduna sun shiga yajin aikin sai Illa-Ma-Sha-Allah.
Da ya ke sanar da fara yajin aiki yau shugaban kungiyar likitocin jihar Joseph Jokshan ya ce hakan ya zama dole ganin irin halin da asibitocin jihar suka shiga.
Joseph yace bayan rashin inganta aikin likita da gwamnatin jihar taki yi, asibitocin jihar duk sun rugurguje inda wasu ma ba za a iya aiki a cikinsu ba.
Ya ce dama can maneji likitocin suke yi amma abin yanzu ya kai makura.
Joseph ya koka rashin kayayyakin aiki a asibitocin da kuma rashin ma’aikata.
” Wasu likitoci da dama sun isa a yi musu karin Girma amma shiru kake ji ba a ma ko maganar.
Daga karshe ya roki jama’ar jihar da suyi hakuri da wannan mataki da suka dauka cewa hakan ya zama dole sannan yana rokonsu da su mara musu baya domin kai wa ga cin nasara.
Discussion about this post