Jami’an Kwastan sun kama motocin sumogal 3,665 daga 2015 zuwa yau, kamar yadda Shugaban Hukumar, Hameed Ali ya bayyana. Ya kuma ce an samu tara kudin shiga na ‘kwastan duti’ har sama da naira bilyan 13.
Ali ya kara da cewa a cikin 2015 an kama motoci 1,917, yayin da aka tara naira bilyan 3.856, sai kuma cikin 2016 da aka cafke motoci 1,483, aka tara kudin ‘kwastan duti’ naira bilyan 2.683.
Shugaban na Hukumar Kwastan ya yi wannan jawabi ne ranar Alhamis a wurin wani taron “Neman Mafita daga Matsalar Sumogal da Illolin sa”, a Abuja.
Ali ya ce a cikin 2017 an kama motoci 265, amma kuma an karbi haraji na naira bilyan 6.625. Ya na mai karawa da cewa an samu makudan kudin da aka samu a 2017 wanda ya haura na shekaru biyun baya, saboda akasari duk manyan motoci ne masu tsadar gaske aka kama.
Idan ba a manta ba, cikin 2017 din nan, rundunar jami’an hana fasa-kwauri sun cafke wasu motocin alfarma har guda 15 da ka shigo da su kasar nan ta barauniyar hanya. Dukkan motocin kuma masu sulken hana harsashi shiga motar ne.
Ya ce daga cikin motoci 18 da aka kama cikin 2017, 13 masu sulke ne, wadanda 10 daga cikin su ba su da takardun kwastan.
Daga nan sai ya yi tsokaci da cewa Nijeriya ta na shigo da kashi 70 bisa 100 na abubuwan bukatun ta na yau da kullum, alhali kashi 45 bisa 100 na kayayyakin duk ta hanyar sumogal ake shigo da su.