Asusun tallafa wa kanan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF tare da ma’aikatar ruwa na jihar Borno sun hada guiwa wajen kafa wuraren wanken hannu a makarantun da yaran ‘yan gudun hijira ke karatu.
Sun yi haka ne domin kawar da cutar kwalara a jihar musmman yadda cutar ta yi ajalin yara 59 a sansanonin ‘yan gudun hijra dake jihar.
Da yake kaddamar da wurin wanken hannu a daya daga cikin sansanonin jihar Jami’in hukumar UNICEF Geoffery Ijumba ya ce hakan zai taimaka wajen kare yara kanana daga kamuwa da cutar kwalara.
” Fanfunan da muka kakkafa za su yi aiki da hasken rana da kuma na wutan lantarki domin samar da ruwa a kowani lokacin da ake bukata.”
Da take tofa albarkacin bakinta kwamishinan ruwa na jihar Barno, Zainab Gimba ta ce jihar Borno na kokarin ganin ta samar da ruwa yadda ya kamata a sansanonin jihar ta hanyar haka rijiyoyin burtsatse.