Kotu ta yanke ma wasu matasa da aka kama suna gararamba a gari Bulala shida-shida

0

Kotun dake sauraron kararraki dake unguwan Karmo a Abuja ta kama wasu mataza maza uku da laifin yawan banza a wasu lunguna dake wurin kusa da wajen shakatawa na‘Hill Top Garden ’ kusa da Kasuwar Wuse.

Wacce ta shigar da kara Florence Ayhioboh ta sanar da kotun cewa ‘yan sandan dake aiki a unguwan Utako ne suka kama su. Wadanda aka kama kuwa sune Daniel Lucky, Aliyu Ahmed da Badiru Lawal.

Matasan dai basu bada wani takamammen hujja da ya sa suke ta galantoyi a titunan Abuja ba da tsakar wannan dare sai dai sun nemi ayi musu Abuja cewa baza su kara yin haka ba.

Alkalin kotun Abubakar Sadiq ya yanke musu hukuncin kowa ya lallasa masa jiki da dorina sau shida shida da sharadin ba za su sake aikata hakan ba.

Share.

game da Author