Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa ta na jiran umarnin kotu ne kawai, domin ta san mataki na gaba da za ta dauka domin fara shirin yi wa Sanata Dino Melaye kiranye.
Shugaban Hukumar ne, Mahmud Yakubu ya bayyana haka a ranar Talata, yayin da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja.
Melaye dai ya na ta kai-gwauro-kai-mari wajen kokarin ba a yi nasarar yi masa kiranyen da ‘yan mazabar ta sa daga Jihar Kogi ta Yamma ke kokarin yi masa ba.
Sun aika da takardun korafi da neman yi masa kiranye ne ga INEC tun ranar 23 Ga Yuni, 2017.
Yayin da shi kuma Dino ya falfala a guje zuwa Babbar Kotun Tarayya, da nufin hana a yi masa kiranye.
Idan ba a manta ba, jami’an hukumar zabe sun dira Majalisar Tarayya a ranar Talatar makon jiya, inda su ka nemi damka masa takardan korafin da ‘yan mazabar sa ke yi masa.
Dino ya ki tsayawa ya karbi takardun, maimakon haka, sai ya gudu, ya na mai cewa wai lokacin da dokar kasa ta gindaya adadin ranakun sun shude, wato an haura kwanaki 90 kenan.
Guduwar da Melaye ya yi ce ta sa jami’an INEC su ka jibge masa buhunan takardun korafe-korafen da wadanda su ka zabe shi tun farko ke yi masa.
Yanzu dai hukumar zabe na jiran umarnin Babbar Kotun Tarayya ne.
Discussion about this post