Akalla kauyuka 12 ne suka amince su saka hannu a takardan yarjejeniyar sulhu a tsakaninsu a jihar Filato.
Wakilan kauyukan tare da wata kungiya mai zaman kanta ‘Humanitarian Dialogue’ ne suka amince akan hakan don hana rikicin da ke yawan tashi a jihar.
Wakilan kauyukan sun amince a jawo hankalin Sarakunan gargajiyya da shugabannin addini kan wayar da kan mutane mahimmancin zaman lafiya.
Kungiyar ‘Humanitarian Dialogue’ta ce hakan da kauyukan suka yi ya yi daidai saboda hakan zai taimaka wajen samun dawwamammiyyar zaman lafiya a yankunan.
Wadanda suka wakilci Kauyukan sun hada da Agwon Isha, Aminu Zang, Salihu Umar, Zacch Nwankpa, Bankole Falade, Joseph Jemkur da wakiliyar kungiyar ‘Humanitarian Dialogue’ Alice Nderitu.
Discussion about this post