Wani Mai taimakawa gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, Abudulkadir Nasir ya ce gwamnatin jihar ta dauki nauyin horas da matasa 500 mazaunan jihar dake sana’ar kasuwanci kan dabarun da zasu iya bi don ririta ribar cikin su domin bunkasa cinikayya a jihar.
Abdulkadir ya sanar da haka ne wa manema labarai a taron horas da ‘yan kasuwa da aka fara a jihar ranar Laraba.
Abdulkadir Nasir ya kara da cewa bayan an kammala horas da su gwamnati zata raba musu takardun shaidar kammala samun horon wanda zai taimaka musu wajen samun jari daga babban bakin Najeriya,CBN.