Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce abin takaici ne ace wai malamim da ke Karantar da dalibi a makaranta bai iya cin jarabawar dan aji hudu na firamare ba kuma wai yana Karanta da dalibi har na sama da aji hudu.
El-Rufai ya koka da yadda aka debi malamai a jihar a baya cewa siyasa aka mai da shi ba wai don a ba yara ilimi ba.
Ya ce gwamnati ta shirya wa malaman jihar su 33,000 jarabawa amma kashi 66 sun kasa cin jarabawar.
Gwamnan ya kara da cewa za a sallami dakikan malamai 20,000 sannan gwamnati za ta dauki sabbin malamai 25,000 kwararru kuma sabon jini domin Karanta da yara a makarantun gwamnatin a jihar.
Ya ce baza a bar makarantun kananan hukumomi ba inda malamansu ke fama da dalibai da yawa kuma babu isassun malamai.
Ya ce za a kara yawan malamai a makarantun da ke kauyuka.
Gwamnan El-Rufai ya fadi wadannan matsaloli ne da yake zantawa da jami’ an bankin duniya da suka kawo masa ziyara a gidan Sir Kashim Ibrahim dake Kaduna.