Shugaban hukumar kwastam Hamed Ali ya ce cikin dalilan da ya sa gwamnatin Buhari ta kasa cika alkawurran da ta dauka wa mutane shine raba ma wadanda ba ‘yan jam’iyya bane mukamai da akayi aka yi watsi da wadanda suka wahala kuma ‘yan asalin jam’iyyar APC.
Hameed Ali yace kusan kashi 50 bisa 100 na wadanda aka nada ‘ yan PDP ne kuma sune ke cin karen su babu babbaka a wannan gwamnati.
Ya kara da cewa hakan da akayi ya sa gwamnatin ta kasa samun seti har yanzu domin da gangar ne suke hargitsa ta don kada ta sami nasara.
Shugaban kwastam din ya fadi haka ne da yake bude sabuwar ofis din ‘ BuharSupport Organisation’ a Abuja wanda jaridar The Nation ta ruwaito.
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya bi sahun Ali in da ya ce tabbatar da wannan ikirari da Ali ya yi kan wannan gwamnati.
Ya ce duk wadanda suka sadaukar da komai nasu don ganin an sami nasara ba su ko kusa da wannan gwamnati. Ya ce abin fa da sake.
Wani mai yin sharhin siyasa, Gbola Oba ya ce ko a lokacin Manzon Allah (SAW) idan aka dawo daga yaki ita kanta ganimar da aka samo ba kowa ne ake baiwa ba. Wadanda suka kara da makiya ne ke ci da samun kaso mai tsoka a ganimar.