Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya karyata cewa da ministan mai Ibe Kachikwu yayi wai an buga karmakarma na wata kwangilar mai da aka bada na dala biliya 25 a wasikarsa cewa babu wata kwangila mai kamar haka.
Osinbajo ya ce kamfanin mai na kasa ya tantance kamfanonin da za a basu lasisin shigo da mai ne amma babu kwangila da aka bada na kudi kamar yadda ministan ya fadi a wasikarsa.
“ Dalilin haka bai dace ba ace wai ministan ya fadi cewa wai an bada kwangila na irin wadannan kudade ba bayan ba haka bane.
“ Sannan kuma tabbas na saka hannu a wasu yarjejeniya da ya shafi harkar mai amma ba kwangila muka bada.
“ Duk ababen da muka sa wa hannu sun shafi yarjejeniya ce na siya da siyar da mai amma ba kwangila da ya shafi yin amfani da dukiyar talakawa ba. Babu maganar kudi a ciki.”
“ Duk abin da muka yi ya shafi tantance wasu kamfanoni ne da za suyi aikin shige da ficen mai.
“ Saboda haka ba ayi wa gwamnati adalci ba cewa da akayi wai sun dibi kudin talakawa ne suka raba kwangilolin mai.
Laolu Akande na ofishin mataimakin shugaban kasa ne ya sanya wa wannan takarda hannu.
Discussion about this post