JOHESU ta janye yajin aiki

0

Hadadiyyar kungiyyar ma’aikatan kiwon lafiya JOHESU ta janye yajin aikin da ta shiga tun a ranar 20 ga watan Satumba.

Kungiyar ta janye yajin aikin ne bayan amincewa da alkawurran da gwamnati tayi mata a tattaunawar da suka yi a Abuja.

Shugaban kungiyar Biobelemoye Josiah ya yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya da su koma kan bakin aikin ranar Laraba.

Ya kuma ce kungiyar za ta ci gaba da tattaunawa da gwamantin ranar Talata domin daukan tsayayar matsaya.

Share.

game da Author