Jihar Kano ce kan gaba a yawan malaman da basu kware a aikin malunta ba -TRCN

0

Shugaban Cibiyar kula da aikin malaunta ta kasa Josiah Ajiboye ya ce jihar Kano kawai na da yawan malamai sama da 25,000 da basu da kwarewa a aikin malunta.

Ajiboye ya fadi haka ne a Abuja wajen taron da kayi don tattaunawa kan yadda za a inganta aikin malunta a kasarnan.

“ Sama da malamai 300,000 cikin 700,000 dake karantarwa a makarantun kasarnan basu da kwarewa akan aikin malunta.

Yace jihar Kano ne ke kan gaba waje yawan malaman da basu kware a aikin malunta ba.

Ya kara da cewa cibiyar TRCN na kokarin tura malamai manyan makarantun koyan aikin malunta da kwalejojin kimiyya da fasaha domin gogewa a harkar karantarwan.

Bayan haka ya koka ga yadda wasu jihohi a kasarnan basu damu da jindadin malamai ba in da wasu harta albashi ma ke musu wuyan biyan malamai.

Share.

game da Author