Jawabin Shugaba Muhammadu Buhari A Yau 1 Ga Oktoba, 2017.

0

Ya ku ‘yan Najeriya

Ranar 1 Ga Oktoba ta kasance rana ce ta da mu ka samu babban abin da dan Adam ya fi muradin ya samu, wato ‘yanci.

Najeriya ta samu kan ta cikin wasu mawuyacin halaye a ‘yan shekarun da mu ke ciki, amma duk da ita ranar 1 Ga Oktoba, abar yin murna ce a gare mu.

Rana ce da za mu nuna godiya da hamdala, tuna baya da kuma kara nuna jajircewa da sadaukarwa ga kasar mu.

Kuma rana ce ta tunatarwa. Ya dace mu tunatar da kan mu dajin da muka keto daga 1999 zuwa 2015, lokacin da kasar mu ta koma kan mulkin farar hula.

Duk da cewa a lokutan farashin danyen mai sai da ya kai Dala 100 a kowace ganga guda, kuma a kan rika hako har ganga miliyan 2.1 a kowace rana, abin takaici sai aka yi watsi da wannan gagarimar damar inganta kasar nan, aka rika almubazzaranci, wawura da kuma balle-bushasha da wannan dimbin dukiya.

Haka aka bar mu ba sidi ballantana sadada, ba a amfana wa jama’a wajen inganta ababen more rayuwar su ba.

Gwamnatin APC ta yi kamfe wajen yekuwar dawo da tsaro, saisaita tattalin arziki daga baudaddar hanyar da aka karkatar da shi, yaki da cin hanci, sannan rashawa ba tatsuniya ba ce, da gaske ake yi.

Tilas tashin farko sai an samar da tsaro, an saisaita tattalin arziki, ta yadda za mu daina dogaro kacokan a kan danyen man fetur.

Sai kuma mun yi yaki da cin hanci, wanda shi ne Babban Abokin Gabar Najeriya, Kuma gwamnatin mu na yaki da shi sosai.

A cikin shekaru biyu da su ka gabata, Najeriya ta wanzar da ‘yancin siyasa,
inda wadanda ke rike da mulki a karkashin jam’iyya mai ci su ka rasa mukaman su da dama, ko a gwamnan jiha, ko majalisar jiha da ta tarayya. Inda jam’iyyar adawa ta kwace daga hannun su.

An kuma samu dama da ‘yancin bayyana ra’ayi, wanda dama shi ne gishirin dimokradiyya. Sai dai a baya- bayan nan, ana wuce-makadi-da-rawa da sunan ‘yancin bayyana ra’ayi.(Premium Times Hausa)

Kiraye-kirayen da aka rika yi kwanan nan da nufin sauya fasalin Najeriya, ya bada kofa wasu ‘yan a-fasa-kowa-ya-rasa su ka rika hayagagar a raba kasar nan. To ba za mu taba aminta da kuma kyalewa ana watsa wannan mummunar farfaganda ba.

(Premium Times Hausa) Ina karamin soja da ni aka yi yakin basasa har aka gama ina ciki tsundum. Yakin nan ya haifar da asarar rayuka kusan milyan biyu. Ya kuma kawo asarar dukiyoyi da halin kunci matuka.

“Wadanda ke ta hauragiya da tayar da jijiyar wuyar maimaita Yakin Basasa a kasar nan, ba a haife su kafin 1967 ba. Kuma ba su da masaniyar balbalin-bala’in illar basasar da mu ka shiga.

Girman wasu manyan wancan yanki ya zube a ido na, ganin yadda su ka kauda kai daga yi wa matasan su ‘yan zafin kai kakkausan gargadi da shaida musu bakar wahalar da Yakin Basasa ya haddasa.

Ya kamata wanda ya dandani zafin Yakin Basasa su sanar wa wadanda ba a haifa a lokacin ba, cewa sake tayar da batun basasa wauta ce, ba karama ba.

Kamata ya yi a tattauna wadannan batutuwa ta hanyoyin da dokar kasa ta tanadar a Majalisun Tarayya da na Jihohi. Wadannan su ne doka ta yarda su tattauna batun sauya fasali, ba wasu baudaddun mutane masu wani shiryayuen mugun-nufi ba.

Gwamnati na ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki a yankin Neja Delta domin tabbatar da kyakkyawan tsaro a yankin.

Mu na da kyakkyawan kudirin magance duk wani koke mai ma’ana a yankin.
(Premium Times Hausa)

Sannan kuma gwamnati na godiya da yabawa dangane da kyakkyawan shugabancin da jagororin al’ummar yankin ke tafiyarwa.

Za mu mara musu baya wajen samar da zaman lafiya na dindindin a yankin.

TSARO

A fannin tsaro, dole ‘yan Najeriya su yi shukura da jinjina ga zaratan sojojin Najeriya masu jajircewa wajen shigewa gaba su na fatattakar Boko Haram. A yanzu sun kai Boko Haram makurar kakkabe su, sun boye sai dai su rika kai harin sari-ka-noke kawai a daidaikun wurare.

Najeriya na godiya ga kasashe makwauta da kuma kungiyoyin kasa da kasa wadanda su ka taimaka wajen ganin mun cimma kudirin mu na kakkabe burbushin Boko Haram. (Premium Times Hausa)

Wannan matsalar ta’addanci ta addabi hatta manyan kasashen Turai da wasu yankuna masu ingantaccen tsarin ‘yan sanda, su ma sai da ta’addanci ya zame musu karfen-kafa.

Ba mu bar sojojin mu baya ba wajen inganta ayyukan su, ta habbaka OPERATION LAFIYA DOLE, mun kuma kafa dakarun kai farmakin gaggawa a Arewa maso Gabas. Wannan ne zai kawo yunkurin da mu ke yi na karshen ganin bayan Boko Haram.

Gwamnati na kan kokarin ganin an sako sauran daliban Chibok da ma sauran wadanda ke tsare a Hannun Boko Haram.

Sojoji da sauran jami’an tsaro na bakin kokarin su wajen ganin sun magance matsalar garkuwa da mutane, fashi da makami, rikicin Fulani da manona da sauransu domin kara jaddada tsaro a fadin kasar nan.(Premium Times Hausa)

TATTALIN ARZIKI

Gwamnati na kokarin ganin ta kara fadada hanyoyin inganta tattalin arziki. Ga tsarin bayar da rance ga manoma, wanda na kaddamar tun 1 Ga Nuwamba, 2015. Shirin kuma ya samu gagarimar nasara, ta hanyar:

1- Raba naira biliyan 43.92 da CBN ta yi ga wasu cibiyoyi 13.

2 – Kananan manoma 200,000 daga jihohi 29 na cin moriyar shirin.

3 – An noma wasu amfanin gona har iri 8 a cikin hekta 233,000. Ana noma shinkafa, alkama, auduga, waken-soya, kiwon kaji, rogo, gyada da kuma noman kifi.

Zan so na yaba wa Gwamnatocin Jihar Kebbi, Legas, Ebonyi da Jigawa dangane da gudummawar su wajen samar da shinkafa da kuma takin zamani.

(Premium Times Hausa) Haka kuma ina jinjina wa Gwamnonin Ondo, Edo, Delta, Imo, Cross River, Ogun, Kaduna da Filato dangane da goyon bayan su ha shirin Shugaban Kasa na inganta noman man ja, roba, kashiw, rogo, tumatir da sauran kayan gona.

Ganin yadda mu ka samu yalwar ruwan sama a wannan damina, harkar noma ta samu wani babban tallafi daga Allah Madaukakin Sarki.

Daga Disamba na shekarar da ta gabata zuwa yanzu, wannan gwamnati ta samar da taki sama da buhuna miliyan 7, kuma ana sayarwa a kan Naira 5,500 kowane buhu mai nauyin 50Kg sabanin yadda farashin yake ada.

Baya ga wannan kuma, Ofishin Shugaban Kasa na kan hanyar fara sabon shirin samar da ayyukan yi har 10,000 ga dimbin matasan mu, ta hanyar sa hannun Babban Bankin Tarayya, CBN.

Harkar samarda hasken wutan lantarki ta zama babbar matsala. Ya zuwa Satumba, 12 ga wata, ya yi karuwar da bai taba yi ba zuwa Megawatts 7,001.(Premium Times Hausa)

Mu na sa ran zai karu zuwa Megawatts 10,0000 nan da shekarar 2020. Ina matukar farin cikin shaida muku cewa Aikin Samar da Hasken Lantarki da sauran nau’ukan Makamashi ya kankama a tsibirin Mambilla.

Idan mu ka sake komawa bangaren tattalin arziki kuwa, watanni bakwai kenan a jere ana samun sassaucin farashin kayayyaki.

Naira ta yi tsayuwar tabarya wuri daya, tun daga Fabrairu zuwa yau, ta na N360 a kowace Dala. Sabanin yadda ta ke N525 a baya.

Yanzu tsarin tattalin arzikin mu ya fitar da mu daga matsalar kuncin tattalin arziki.

Domin kara inganta tafiyar wannan gwamnati, Gwamnatin Tarayya ta na ci gaba da tallafa wa jihohi ta hanyoyin:

1 – Ba su lamuni daga asusun kudaden rarar man fetur.

2 – Tallafa wa hidindimun inganta kasafin kudaden su.

3 – Tallafa musu da kudaden daidaituwar kudaden gudanar da ayyuka wa jihohi da kananan hukumomi.

Gaba gaba daya jimillar kudaden sun kai Naira Tiriyan 1.642.

An yi haka ne domin taimaka wa jihohi su rika biyan albashin baya da ma’aikata ke bi bashi, fansho da sauran kananan ayyuka, wadanda su ka nemi durkushewa a baya.

An kuma kashe naira biliyan 500 wajen ciyar da dalibai, shirin N-Power da kuma shirin samar da muhalli.

RASHAWA DA CIN HANCI:

Ya ku ‘yan Najeriya, yaki da cin hanci da rashawa ba abu ne na sha-yanzu-magani-yanzu ba. Dama mun san wadanda su ka wawure dukiyar kasar nan, ba za su zura ido mu yake su ba, su ma su na nan su na yakin mu. Musammam ta hanyoyin yi wa shari’u dabaibayi da kuma kutunguila ta siyasa. (Premium Times Hausa)

Amma duk da haka, mun dauki alwashin kawar da cin hanci da rashawa a harkokin mu da na sha’anin tafiyar da gwamnati.

Dangane da haka Gwamnati ta fito da:

1 – Kara wa masu gabatar da kara karfi aiki.

2 – Samar da hanyoyin tattara bayanai.

3 – Aiwatar da shirin kwato dukiyar da aka sace ta hanyar hanzarta shirin.

4 – Samar da Asusun Bai Daya, TSA.

5 – fito da shirin fallasa barayin gwamnati, wato hura usur.

Da sauran tsare-tsare masu yawa.

An nada Babban Mai Shari’a, Ayo Salami a matsayin shugaban kwamitin shari’ar rashawa da cin hanci. Gwamnati na fatan samun nasara sosai daga wannan kwamiti.

Ina jinjina wa Majalisar Tarayya, da fatan za su maida hankali wajen tabbatar da amincewa da dokar hukunta maciya hanci da rashawa.

Ina kira ga ‘yan Najeriya da su sa hannu biyu wajen yaki da cin hanci da rashawa. A rika kauce wa bayarwa da karbar rashawa. Sannan kuma a rika hura wa maciya rashawa usur ana tona su. Ta haka ne za mu magance matsalar.

Yayin da muka shiga zangon cikon shekaru biyu na gwamnatin mu, mun kudiri aniyar hanzarta ayyuka da magance wasu kalubale da shawo kan matsaloli.

Na gode kwarai, a yi hutun ranar ‘yanci lafiya.

Allah ya albarkaci Najeriya.

Share.

game da Author