Jam’iyyar APC ta jinjina wa shugabancin Oyegun

0

Jiga-jigan jam’iyyar APC da suka halarci taro na musamman da suka yi a fadar shugaban Kasa Muhammadu Buhari sun jinjina wa jagoranci shugaban jam’iyyar John Oyegun.

Shugaban Kungiyar gwamnonin Najeriya, gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari da yake zantawa da ‘yan jarida bayan kammala taron yace gabadayan su sun amince da yadda Oyegun ke tafiyar da jagorancin jam’iyyar.

Wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC sun gudanar da zanga-zanga a ofishin jam’iyyar dake Abuja suna kira GA shugaban jam’iyyar ya sauka daga kujeran shugabancin jam’iyyar.

Wasu na ganin cewa tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu na da hannu a shirya wannan zanga-zanga ganin yadda suke zaman doya da manna shi Oyegun.

Tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata Bukar Abba ya ce wanna ganawa da suka yi da shugaban kasa nuni me cewa jam’iyyar APC na nan tsintsiya madaurin ki daya.

Sai dai Kuma gudu ba hanzari ba, ba a ce ana tuya an manta da albasa ba domin ba a ga wulkawar Wazirin Adamawa ba, Atiku Abubakar a ko daya daga cikin wadannan tarorruka da ake tayi da ‘yayan jam’iyyar a ofishin shugaban Kasa ba.

Da muka nemi ji daga bakin darektan yada labaran tsohon mataimakin shugaban kasan Paul Ibe, ya ce Atiku baya Kasa Najeriya ne.

” Makonni 6 Kennan Atiku ba ya Najeriya. Ba ya Kasar tun kafin a fara jerin wadannan ganawa da shugaban kasa.

Share.

game da Author