Hukumar Hana Sha Da Safarar Kwayoyi, NDLEA, ta bayyana cewa, ta lalata gonakin da aka shuka tabar wiwi a jihar Osun.
Sanarwar da Shugaban Hukumar na Jihar, Samuel Egbeola ya bayar a jiya Asabar, ya ce sun kona gonakin ne a ranar Alhamis da ta gabata.
Da ya ke karin bayanin yawan tabar wiwi din da kuma fadin gonakin, Egbeola ya ce sun kai fadin filin kwallo har guda 74.
Ya kara da cewa sun gano wadannan maka-makan gonakin ne bayan da wani mai kishin kasa ya kawo musu kwarmaton inda ake noman wiwi din, a Ikeji Affeji cikin jihar.
A karin bayanin sa, ya ce sun kama mutane biyu da aka samu su na aiki a cikin wata gonar. Su na tsare ne inda su ke bada bayanin mamallakan wannan katafariyar gona.
Ya kuma ce sun kama buhuna goma a wani samamen wani wuri daban, wadanda ya ce sun kai nauyin kilogiram 107.
A karshe ya ce ba za su gaji ba wajen kokarin su na ganin sun kakkabe muggan kwayoyi a kasar nan.
Discussion about this post