Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa hukumar sa ta karbo sama da naira biliyan 30 sakamakon tsarin dabarar fallasa barayin gwamnati da aka fi sani da hura usur.
“Daga tun da aka fara tsarin hura usur zuwa yau, mun samu daruruwan rahotannin kwarmato wadanda mu ka bi, kuma mu ka yi nasanar samo kudade masu yawa.
Magu ya yi wannan jawabi ne jiya Alhamis yayin kaddamar da shirin Hura Usur na gadan-gadan, a Abuja.
Ya ce sun karbo naira milyan 5.27; Dala miliyan 53.22; Fam 21,222 da kuma Yuro 547,730.
Kungiyar AFRICMIL ce ta shirya taron da hadin guiwar Gidauniyar MacArthur.
Magu ya kara da cewa EFCC ta fito da kofar jawo jama’a a jika, wato ga wanda duk ke da wani bayanin da za a iya bi domin a kwato kudaden sata daga hannun jama’a, amma fa sai idan ya tabbatar da sabihancin bayanan na sa.
Wannan tsari da aka shigo da shi, wato CORA, zai taimaka kwarai wajen karewa da bayyana ko wane fallasa wani har aka samo kudin sata daga hannun barayin gwamnati.
“Duk da haka, mu na taka-tsantsan don kada masu kokarin yi wa tsarin kafar– ungulu su shigo su lalata shirin.”
Discussion about this post