A kokarin ta na rage radadin talauci, Hukumar Tara Zakka ta Jihar Zamfara, ta raba naira milyan hudu ga mabukata a cikin Gusau.
Shugaban Hukumar Muhammad Dan’Alhaji ne ya bayyana haka a jiya Alhamis, ya na mai cewa raba kudaden ga mabukata daban-daban ya biyo bayan ganin cewa bayar da zakkar gare su zai inganta rayuwar su.
Ya ce dama daya daga cikin manyan dalilan da ke sa ana tarawa ko karbar Zakka a Musulunce, shi ne shi ne a inganta jin dadin rayuwar mabukata.
“Mun fahimci cewa talakawa, mabukata da sauran masu karamin karfi na matukar bukatar tallafi, shi ya sa mu ka raba musu kamar yadda mu ka yi.
” Banda wannan kuma, mu na da tsare-tsare da dama wanda mu ke kai agaji ga jama’a ta hanyar lafiya, ilmi, inganta kananan kasuwanci, taimakawa da matsuguni da sauran su.”
Ya roki wadanda su ka karbi tallafin zakkar da su yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace musu.