Shugaban riko na karamar hukumar Riyom jihar Filato Emmanuel Jugul ya ce mutane biyu sun rasa rayukansu sannan biyu sun sami runuka a jikinsu sanadiyyar harin da aka yi a kauyen Jol a cikin daren jiya Talata.
Ya ce sun kai mutane biyun asibiti.
Emmanuel Jugul ya sanar da haka ne yayin da gidan jaridar PREMIUM TIMES ta yi hira da shi ranar Laraba.
Ya bayyana cewa sanadiyyar tsinto gawan wani bafulatani ne da a ka ganin a kauyen Jol ya tada wannan rikicin.
” A makon da ta gabata mun kai karan bacewar wani bafulatani wajen jami’an tsaron dake kauyen wanda ‘yan cigiyan da muka aika suka tsinto a wannan kauyen shekaran jiya.”
A takaice dai tun da rikicin kauyukan jihar Filato ya fara mutane 44 ne suka rasa rayukkan su a cikin wata daya daya wuce.
Discussion about this post