Gwamnonin Najeriya sun roki shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya basu cikon kudin tallafi na ‘Paris Club’ kamar yadda yayi alkawari kafin 2018.
Shugaban gwamnonin Najeriya, AbdulAziz Yari ne ya fadi haka da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan sun fito daga ofishin shugaban kasa bayan ganawa da suka yi.
“ Mun ziyarci Shugaban Kasa ne domin mu tuna masa cewa ya kamata ya bamu sauran cikon kudin tallafi na ‘Paris Club’, wato kashi hamsin da ya rage.”
Gwamnonin wanda Yari ya jagoranta zuwa ofishin shugaban kasan sun kara da cewa sun yi haka ne ganin cewa 2018 ya karato, cewa samun kudin zai taimaka musu wajen gudanar da manyan ayyuka a jihohinsu da kuma samun kudaden da za su gudanar da ayyukan gwamnati.