Sakataren yadda labarai na shirin bada agaji a fadan shugaban kasa Nura Sani yace gwamnatin tarayya ta samar da Naira miliyan 229,640,000 domin tallafawa mata 22,962 a jihar Jigawa.
Nura Sani ya ce gwamnati ta yi haka ne a shirin tallafa wa talakawa domin kawar da talauci a kasar nan wanda ake kira da ‘Conditional Cash Transfer CCT’.
Ya ce sun raba wa talakawa dake kananan hukumomi 9 a jihar wanda ya hada da Auyo, Guri, Gwiwa, Jahun, Kaugama, Kiyawa Miga, Roni da Taura.
” Mun zabo matan da muke tunani sun fi fama da talauci daga mazabu 3 daga cikin wadannan kananan hukumomi 9 a jihar.”
Nura Sani ya ce a wannan rabon kashi 30 na talakawan dake kananan hukumomi 27 a jihar ne suka sami tallafi sannan za su ci gaba da rabon kudin a karo na biyu domin sauran talakawan dake mazaba 15 su samu.
Ya ce sharadin samun wannan tallafin ya hada da saka yara a makarantun gwamnati da ziyartan asibiti a kai-akai.