Gwamnatin Najeriya ta maka sanata Misau a Kotu

0

Gwamnatin Najeriya ta maka tsohon dan sanada kuma sanata Isah Hamma Misau A kotu saboda korafin da yayi a zauren majalisa cewa wai Sifeton ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya dirka ma wata ‘yar sanda ciki.

Gwamnatin Najeriya ta ce ta shigar da karar ne ganin cewa ababen da Misau fadi ba dadidai bane.

Kamar cewa da yayi wai ‘yan sanda sukan biya naira miliya 2.5 domin samun karin girma na musamman. Sannan kuma wai kamfanonin mai, bankuna da otel suna biyan sifeton ‘yan sanda naira biliyan 10 cin hanci domin samar musu da kariyar ‘yan sanda.

Wani dalilin kuma shine wai Sanata Misau ya mika takardun karya ne ga hukumar Zabe wajen neman tsayar da shi dan takarar kujerar Sanata a mazabar sa.

Share.

game da Author