Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da cewa ba kamar yadda ake ta yada bayanan karya ba cewa wai da gangar ne ta ke neman ta hana shan barasa a jihar, ta ce doka ce wanda akayi kuskuren cire wani sashi da ya ke da alaka da haramta hakan ga musulman jihar ne kawai.
Majalisar dokokin jihar ta amince da wannan doka na jihar wato’Penal Code’ da ya haramta hakan in da tayi kuskuren cire ga musulmai kawai ya zama ga kowa da kowa.
Jin hakan ke da wuya jama’a suka fara fadin albarkacin bakin su game da haka inda suke kushe wannan doka cewa ya saba wa ‘Yanci ‘yan Adam.
Wani jami’in gwamnatin jihar ya ce sashe na 382 da ya haramta hakan ya tsaya ne ga musulman jihar amma ‘yan majalisa sukayi kuskuren cire musulmai suka barshi kan kowa da kowa.
Duk da cewa sashi na 381 da 382 ya haramta mutum ya sha barasa ya buga na babu gaira babu dalili.
Ya kara da cewa da ganin haka sai gwamnati ta sake rubuta wa majalisar sabuwar wasika kan haka domin gyara wannan kuskure a dokar.
Jami’in ya ce wasu ne kawai suke so su yi amfani da kuskuren da akayi domin samar da abin fadi tsakanin mutane.
Samuel Aruwan ya ce gwamnatin jihar ba za tayi wani abu da zai tauye wa mutanen jihar ‘yancin su ba, sai dai wata jami’ar hudda da jama’a a majalisar dokokin jihar ta karyata gwamnatin cewa har yanzu bata aiko wa majalisar neman gyara wannan sashe na doka ba.