Gwamnatin Ebonyi za ta raba wa tsagerun IPOB naira 250,000 kowane

0

Gwamnatin Jihar Ebonyi ta fara rajistar tsagerun IPOB na jihar domin ta san adadin su, kuma ta a jiya musu sana’o’i tare da,ba su jarin dogaro da kai.

Kwamishinan Inganta Tattalin Arziki da Samar da Aikin Yi na jihar, Uchenna Orji ne ya bayyana haka jiya Laraba a Abakaliki.

Gwamnatin ta ce wadannan matasa na jihar, romon-kunne aka yi musu aka rude su suka shiga kungiyar Biafra.

Kwamishinan ya ce ana ci gaba da aikin yi musu wannan rajista ce a kananan hukumomin jihar 13. Ya ce an kudiri aniyar maida matasa nagari, a kawar da su daga aikata laifuka a cikin al’umma.

Sannan kuma ya kara da cewa a za yi wannan rajista ce har ga ‘yan IPOB ‘yan asalin Ebonyi mazauna Jihohin Sokoto, Kaduna, Anambra da kuma Lagos da sauran garuruwa.

Ya zuwa yanzu dai ya ce an rigaya har an yi wa matasa 3000 rajista. Ya kara da cewa za a samar wa matasa 12,000 aiki ta hanyar raba musu naira 250,000 kowane domin ya kama sana’ar dogaro da kan sa.

Wannan tallafi a cewar kwamishinan, ba a kan matasa maza kadai zai tsaya ba, har ma da mata masu tarin yawa.

Orji ya ce matasan nan ba su ma san matsalar kan su ba, balle ta kasar nan. Nnamdi Kanu ne ya ribbace su, shi kuma ya gudu ya bar su. Idan ba a saka su kyakkyawar hanya ba, to za su zama ba nan, ba can.

Share.

game da Author