GWAMNATIN BUHARI A KAN SIKELI: ’Yan Nijeriya sun ce gwamnatin tafiyar hawainiya ta ke yi

0

Duk inda ‘yan siyasa su ke, ba ka raba su da alkawurra ga al’umma, musamman lokacin da su ke neman a zabe su. PDP ta yi na ta a cikin shekaru 16 an gani.

Da dama sun mika wuya ga Muhammadu Buhari a matsayin wanda zai ceto su ko ya ceto kasar nan daga tabarbarewar da ake gani ta yi a karkashin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Jama’a da dama sun bayyana ra’ayin su, kamar dai yadda wani masanin harkokin yau da kullum. Ya yi nasa bayanin a wurin taron CDD, wata cibiyar inganta turbar dimokradiyya da aka gudanar ranar Juma’a a Abuja.

“Mu na dai da gwamnatin dimokradiyya kawai zan iya cewa a yanzu, amma fa gwamnatin ‘yan bankaura kawai. An zabe su saboda ana cewa wai gwamnatin Goodluck Jonathan gurbatacciya ce. Amma kuma abin da ke faruwa a yanzu ai kowa na gani. Gwamnatin Buhari tafiyar hawainiya ta ke yi wajen aiwatar da tulin alkawurran da ta yi wa jama’a.’’ Inji tsohon Shugaban Jami’ar Abuja, Farfesa Nuhu Yaqub.

“Kwanan nan ya nada kwmishinonin zabe na jihohi 12. To me ake jira da na sauran jihohi 16?”

Idayat Hassan wanda ita ce daraktan cibiyar ta ce Buhari ya yi kwanaki 881 a kan mulki. Amma har yanzu batun cin hanci, rashawa da matsalar tsaro fa na nan.

Ta kara da cewa gwamnatin Buhari ba ta wani abin a zo a gani idan aka yi la’akari da irin yadda a farko aka zaci idan ya hau mulki zai yi.

Shi ma daraktan OSI na Afrika ta Yamma, Jude Ilo, ya ce Buhari ya ba shi kunya ta hanyar yadda sau da yawa ya ke take umarnin kotu.

Yawancin wadanda su ka yi bayani da sauran masu fadar ra’ayin su, sun tafi a kan cewa gwamnatin Buhari ba ta bai wa marada kunya ba. Sai ma tafiyar hawainiya da ta ke yi.

Share.

game da Author