Gwamnati ta raba maganin cutar Kwalara a sansanonin ‘yan gudun hijira

0

Wata jami’ar hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa NCDC Nanpring Williams ta ce akalla mutane 184 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da cutar kwalara a shekarannan a jihohi 8 a Najeriya.

Nanpring Williams ta sanar da hakan ne a taron wayar da kan mutanen kan mahimmancin tsaftace muhalli.

Ta ce mutane 8,241 ne daga jihohin Zamfara, Kwara, Borno, Lagos, Oyo, Kebbi, Kaduna da Kano suka yi fama da cutar a wannan shekara.

Nanpring Williams ta ce dalilin haka ne hukumar NCDC ta raba magungunan wa mutane 34,815 dake zama cikin sansanonin Muna da Mafa a jihar Borno.

Ta kuma ce ma’aikatan kiwon lafiyansu za ta ci gaba da gudanar da bincike domin samo hanyoyin dakile yaduwar cutar nan gaba.

Share.

game da Author