Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike, ya gana da wasu ‘yan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo da Sergio Ramos jiya a birnin Madrid, kasar Spain.
Gwamnan ya kuma gana da jami’an kungiyar ta Real Madrid, inda su ka tattauna yadda kungiyar za ta kafa wata cibiyar rainon ‘yan wasa yara kanana a Jihar Ribas.
Kwamishinan Harkokin Wasannin jihar Boma Iyaye ne da tsohon dan wasan Nijeriya, Adokiye Amiesimaka suka rufa wa gwamnan baya yayin wannan ziyara da suka kira mai dimbin tarihi.
Mataimakin Shugaban Kungiyar Real Madrid FC, mai kula da harkokin wasanni, Mista Kazma da wasu jami’an na Madrid ne su ka kewaya da tawagar Wike inda suka gane wa idon su wuraren da Real Madrid ke motsa jiki da atisayen wasan kwallo.
Yayin da Wike ke ganawa da Ronaldo da Ramos, ya shaida musu cewa makasudin kafa Real Madrid Academy a jihar Rivers, shi ne domin a raini yara da a nan gaba za su zama wasu fitattun da za a san su a duniya, nan ba da dadewa ba.
A yau Talata ne kuma Wike zai gana da Shugaban Real Madrid gaba daya, Florentino Perez.
Discussion about this post