El-Rufai ya ziyarci Tafa

0

Gwamnan jihar Kaduna ya ziyarci garin Tafa, dake karamar hukumar Kagarko, jihar Kaduna.

Gwamnan ya tafi garin Tafa ne domin ziyarar gani da Ido na hadarin tankin Mai da akayi jiya a garin.

Wata tankin Mai dauke da fetur ta kama da wuta a garin Tafa inda wasu mutane uku suka rasa rayukansu, wasu Kuma suka jikkita.

Banyan haka Kuma gidaje da dukiyoyin mazauna garin da yawa sun salwanta a sanadiyyar wutan.

Gwamnan El-Rufai ya yi juyayin abin da ya faru sannan Kuma ya Kai ziyarar duba ina aka kwana a aiki da gwamnati ke yi na gina sabon tashan manyan motoci a garin.

FB_IMG_1507503058667

Share.

game da Author