Tsohon Shugaban Hukumar Raba Kudade ta Tarayya, Hamman Tukur, ya bayyana cewa haramun ne a rika raba kudade ga gwamnatin jihohi da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi domin ceto su daga wani hali da suka jefa kan su.
Tukur ya bayyana wannan kakkausan kalami ne ga mujallar ‘Economic Confidendial’ a ofishin sa na Kaduna a wata tattaunawa da ya yi da mujallar a yau litinin.
“Buhari ya na kwasar kudade ya na dibga wa jihohi da sunan kai musu daukin ceto.
Wa ya ba shi wadannan kudaden? Ta ya aka yi ya iya kai hannun sa cikin asusun gwamnati? Wa ya ba shi ikon ba su kudin? Shin Majalisar Tarayya ta ga kudaden a cikin kasafin shekarar da aka fitar da kudaden?
Idan har aka fitar da kudaden kafin a amince masa da ya fitar da su, to ya aikata babban laifi.
“Kuma ma wai shin wa ya ce wata jiha ta je ta tsiyace ko ta talauce ba ta da ko sisi? Wa da wa ya sace kudaden da ake ba su na halaliyar su a kowane wata?
“Kamata ya yi Buhari ya fara tambayar gwamnonin ina suka kai kudaden da ake ba su? Doka dai ta ce ko ma daga ina ake samun ribar kudin da ake bai wa jihohi da sunan agaji, to haramun ne a raba su ba tare da sun shiga asusun gwamnatin tarayya ba.
Tukur na so ya nuna cewa, to muddin kuma aka sa kudin a cikin asusun tarayya, to haramun ne Buhari ya gabza ya rika bai wa jihohi da sunan za su biya albashi ko cike wani gibi ba tare da cewa kudin na cikin kasafin kudi ba.
Tukur ya kuma tunatar da cewa sun hana Obasanjo ya yi irin wannan asarkalar a lokacin da ya ke aiki a karkashin gwamnatin sa.