Mambobin kungiyar direbobin motan Haya 1500 ne a jihar Ribas suka canza sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP a jihar Ribas.
Shugaban kungiyar Ndamati Amadi ne ya sanar da haka da yake jagorantar masu canza shekar zuwa ofishin jam’iyyar a jihar.
Ya ce sun yi haka ne ganin yadda gwamnan jihar Nyesom Wike ya mai da hankali waje ganin ya gyara jihar.
“ Ganin haka ne yasa dukkan mu muka amince mu canza shekar zuwa jam’iyyar PDP” Inji Amadi.
Discussion about this post