A safiyar Lahadin nan ne shahararren dan damben gargajiya Sanin Gidan Dan Kande daga bangaren Arewa ya buge tsohon abokin adawarsa, Kasimu Mai Kasa daga bangaren Kudu.
An buga damben ne a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja.
Dukkaninsu dai shahararrun ‘yan dambe ne a shekarun baya kafin su yi ritayar dambe fiye da shekaru goma da suka wuce.
Amma a bana, Sani da Mai Kasa tare da wasu tsofaffin ‘yan dambe na Kudu da na Arewa sun dawo ruwa bayan da aka sanya musu gasar cin mota a Kaduna, cikin watan da ya gabata.
Kodayake Sani da Kasimu Mai Kasa sun kara a damben gasa na Kaduna amma ba a samu wanda ya buge wani ba a cikinsu.
A makon da ya shige mai gidan damben Dei Dei, Ali Zuma, wanda shima tsohon dan dambe ne, ya sanar da sanya gasar naira dubu 150 tsakanin manyan yan damben guda biyu.
Wanda ya yi nasara a damben ya samu naira dubu 100 shi kuma wanda aka buge ya samu naira dubu 50.
Kafin taka damben dukkanin gwarzayen damben guda biyu sun sha alwashin samun nasara akan juna.
Kuma sun shaidawa PREMIUM TIMES HAUSA cewa sun dawo taka dambe ne domin gyara sanar da kuma nishadantar da ‘yan kallo.
AbdulAziz Abdulziz na PREMIUM TIMES ne ya dauko mana wannan wasa Kai tsaye daga Dei Dei