Dalilin da ya sa na ke so Jonathan ya halarci kotu -Olisa Metuh

0

Babbar Kotun Tarayya Shiyyar Abuja ta dage zaman sauraron rokon da tsohon sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP, Olisa Metuh, inda ya roki kotu da a umarci tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana a kotun, a matsayin mai bayar da shaida.

Ana tuhumar Metuh da harkallar karba kudi naira milyan 400 daga ofishin Mai Bawa Jonathan Shawara a Harkar Tsaro, Sambo Dasuki.

Metuh, ya ce ya na son bayyanar Jonathan a kotun ne, saboda an tura masa kudin ne a bisa umarnin Shugaban Kasa na wancan lokacin, Goodluck Jonathan.

An dai tura wa Metuh naira milyan 400 ne daga asusun hukumar NSA ne, zuwa asusun kamfanin sa mai suna Dextra Investiment.

Lauyan Metuh ya ci gaba da cewa ai tunda dai tsohon shugaban kasa Goodluck ne ya bayar da umarnin tura wa wanda wanda ya ke karewa kudin, to akwai bukatar a gayyace shi tamin ya bayar da shaida.

Shi kuwa lauyan Dasuki, ya nemi kotu ta dakatar da gayyacar wanda ya ke karewa don ya bayyana a matsayin wanda ake zargi

Share.

game da Author