NNPC: TSUGUNO BAI KARE BA
Jawabi ko martanin da Maikanti Baru ya maida wa Ibe Kachikwu, ya nuna cewa Buhari ne da kan sa ya sa hannun amincewa da kwangilolin harkokin mai na naira biliyan 640, a lokacin da ya ke jinya a Landon, duk kuwa da cewa a dokance ya rigaya ya damka ragamar mulki a hannun Mataimakin sa, Yemi Osinbajo.
KARAKAINAR KAI TAKARDUN KWANGILOLI LANDAN
Baru ya ce Buhari ne ya sa hannun amincewa da akalla kwangiloli biyu, a ranar 10 Ga Yuli, ya sa hannun amincewa da kwangilar Dala Biliyan Daya, sai kuma ranar 31 Ga Yuli, inda ya sa hannu kan yarjejeniyar kwangila ta Dala Miliyan 780.
MAIDA OSINBAJO SANIYAR-WARE
Kwangilolin na naira biliyan 640.8, an bayar da su ne a kan naira 360 kowace dala daya, kuma Buhari ya sa musu hannu ne a lokacin ya na jinya a Landan. Wancan lokaci kuwa bai kamata a ce Buhari ya na gudanar da duk wani sha’ani ko aiki da ya shafi mulki ba, domin ya rigaya ya aika wa Majalisar Tarayya takarda cewa ya damka ragamar shugabanci ga mataimakain sa, Osinbajo.
A lokacin da Buhari ya sa hannu kan wadannan kwangiloli na makudan kudade dai, Osinbajo ne Mukaddashin Shugaban Kasa.
Buhari da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa da na Wakilai ta Tarayya wasika a ranar 9 Ga Mayu, 2017, cewa ya damka mulki a hannun mataimakin sa Yemi Osinbajo, kamar yadda dokar kasa ta tanadar, kuma aka karanta wasikar a zaurukan majalisun biyu.
Buhari ya koma Landan ne a ranar 7 Ga Mayu, 2017, watanni biyu kacal bayan dawowar sa daga tafiya jiyya ta farko, inda ya shafe kwanaki 50 a kasar Ingila.
Dama kuma bayan ya yi waccan dawowar ta farko, sai da ya bayyana cewa ba da dadewa ba zai sake komawa ganin likitocin sa domin su sake duba shi.
Tafiyar sa jinya karo na biyu, Shugaba Buhari ya shafe kwanaki 103 kafin ya dawo ranar 19 Ga Agusta, 2017.
Shugaban NNPC, Maikanti Baru, ya yi abin da Hausawa ke kira ‘tsaftar-biri’ ne a ranar 9 Ga Oktoba lokacin da ya ke maida martani dangane da wasikar da Karamin Ministan Man Fetur, Ibe Kachikwu ya aika wa Shugaba Buhari, cewa Baru na gudanar da kwangiloli ba da sanin sa ba.
ALAKA TSAKANIN BARU DA BUHARI
Dukkan kwangilolin uku dai ta tabbata cewa Buhari ne ya sa musu hannu a Landan, a lokacin da ya ke jinya. An sa musu hannu ne a ranakun 10 da kuma 31 Ga Yuli, 2017. Kwangila ta biyu kwamfanin Chevron aka ba ita a ranar 31 Ga Yuli, sannan sai wata kwangilar ta 10 Ga Yuli wadda aka bai wa kamfanin Shell.
A dukkan takardun bayanan kwangilolin dai akwai sunan Maikanti Baru a matsayin wanda ya bayar da kwangilolin, kuma a matsayin sa na Babban Darakta, wato shugaban NNPC.
Bincike ya nuna cewa kwangilolin da Kachikwu ya taba bayarwa a lokacin da ya na shugaban NNPC, kafin ya sauka ya koma Ministan Mai, Buharin ya amince da su ne a lokacin da ya ke Najeriya.
Amma kuma wadanda ya amince da su a lokacin Baru, duk ya na Landan ne ya musu hannu a lokacin ya na zaman jiyya, kuma ya damka mulki ga mataimakin sa, Yemi Osinbajo.
Kakakin yada labaran NNPC, Ndu Ughamadu, ya ki ya ce wani abu yayin da PREMIUM TIMES ta tuntube shi. Sai dai kuma yayin da aka ce masa shin ba ya ganin haramcin wancan sa hannu da Shugaba Buhari ya yi a Landan, domin ya yi shi ne a lokacin da ba shi ne kan mulki ba?
Sai Ughamadu ya ce: “To sa hannun shugaba dai sa hannun shugaba ne, ko a ina kuwa!”
Kokarin jin ta bakin kakakin yada labaran Shugaban Kasa ya ci tura, haka su ma kakakin Shell Bamidele Odugbesan da na Chevron, Sola Adebawo duk ba su ce komai ba.
Amma shi Odugbesan, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa jami’an gwamnati ne ya kamata su yi magana, ba su ba.
BUHARI DA BARU SUN SHA RUFE DAKI A LANDAN
Akwai sabbin ko boyayyun hujjoji da ke nuna cewa Buhari ya ma sanya hannu kan wasu kwangilolin can a baya lokacin tafiyar sa jinya ta farko, kuma a lokacin ya bayar da ragamar mulki a hannun Osinbajo.
Ranar 2 Ga Fabrairu, 2017, NNPC ta yi sanarwar buga tandar neman kamfanonin da za su sayi danyen mai kai tsaye.
Buhari ba ya nan aka yi wannan sanarwa, domin an fita da shi Landan ne a ranar 19 Ga Janairu, 2017. Bai kuma dawo ba sai cikin Maris, 2107.
Sannan kuma a ranar 19 Ga Mayu, ta shaida wa wasu kafafen yada labarai cewa ta shiga yarjejeniyar kwangiloli da kamfanoni 10, kwangilar kuma ta kai dala bilyan 6. A wannan lokacin ma Buhari ba ya kasar nan, kuma ba Osinbajo ne ya sa wa kwangilolin hannu ba.
RA’AYOYIN MASANA SHARI’A
Da dama na cewa kwangilolin da Buhari ya sa wa hannu haramtattu ne, kuma za a iya kai kara kotu domin a soke su.
Wasu kuma na ganin cewa bai dace Buhari ya yi wannan karankatakaliya ba. Yayin da wasu kuma na cewa ba laifi ba ne, amma kuma ana barin halas ko don kunya.
Discussion about this post