Cutar ‘Monkey Pox’ cuta ce da ta bullo a jihar Bayelsa inda a yanzu haka wasu na nan a killace a asibiti ta musamman domin kamuwa da suka yi da cutar.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Bayelsa Ebitimitula Etebu ya sanar da cewa mutane 11 sun kamu da cutar wanda wasu manyan kuraje ne ke fitowa a jikin wanda ya kamu dashi.
Likitoci sun ce Birai, Beraye da dabbobi ne ke kawo wannan cuta sannan sun bada shawarar cewa mutane suyi hankali da dabbobi da musamman irin na daji, bera da Birai.
Sun ce a yawaita wanke hannaye da sabulu sannan a tsaftace muhalli sannan akau da abubuwan da zai kawo beraye.
Kwamishinan ya kara da cewa ma’aikata kiwon lafiya a jihar na gudanar da duba wasu mutane 49 wadanda ake ganin suma sun yi mu’amula da mutane 11 da suka kamu da cutar.
Daga karshe yayi kira ga mutane da su maida hankali wajen kula da lafiyarsu da na iyalansu sannan su gaggauta zuwa asibiti idan suka ji ba sa jin Dadi.