Wani jami’in Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majlisar Dinkin Duniya Mohammed Muhuiddin, ya ce yawan yaran da basu makaranta a jihar Sokoto ya ragu da kasha 50 zuwa yanzu.
Muhiddin ya ce bayanin rahoton UNICEF na shekarar 2015 ya nuna cewa jihar Sokoto ne tafi yawan yara kanana da basu makaranta, amma yanzu tana kan gaba wajen karancin yara da suke gararamba a titunan kasar nan.
“ A shekara 2015 kashe 69 bisa 100 na yara kanana ne basu makaranta a jihar amma yanzu ya ragu zuwa kashi 34 bisa 100 wanda hakan ya nuna ya ragu da kashi 50 cikin shekara biyu kacal.”
Ya kara da cewa babu abin da yake masa dadi da ya wuce irin nasarorin da aka samu a jihar musamman wajen inganta rayukan kananan yara.
Gwaman jihar Aminu Waziri Tambuwal ya ce jihar za tayi rashin Muhuiddin ganin sabo da akayi da shi da kuma irin gudunmawar da yaba jihar.