Buhari yayi tir da rikicin Filato

0

Shugaban kungiyar Irigwe dake kauyen Nkyie-Doghwro Jihar Filato Sunday Abdu ya ce kimanin mutane 27 daga cikin 29 da suka nemi mafaka a wani aji lokacin rikicin da aka yi a garin ne suka rasa rayukan su inda biyu da suka tsira da ransu.

An zargin cewa wasu sojoji ne suka harbe mutanen.

Da yake hira da manema labarai ranar Litini a karamar hukumar Bassa Sunday Abdu ya ce bai ga amfanin kafa dokar hana walwala ba da gwamnatin jihar ta kafa musamman yadda kashe-kashen ya fara bayan an kafa wannan dokar hana walwalan ne.

Ya kuma kara da cewa rikicin ta shafi kauyuka 7 sannan mutane 41 sun rasa rayukansu a cikin wata daya.

Bayan haka shugaban kungiyar CAN reshen arewacin Najeriya Yakubu Pam ya yi kira ga masu unguwanni da su taimaka wajen samar da zaman lafiya a yankunan su.

Shi kuwa shugaban sojojin da suke aiki a wannan yanki wanda ake kira da ‘Operation Safe Heaven’ Anthony Atolagbe yace sojin Najeriya za ta gudanar da bincike akan rikicin musamman akan yadda ake zargin sojoji da aikata kisan gilla a yankin.

‘‘Za mu gudanar da bincike akan duk sojojin da suke aiki a wannan yankin’’.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a nashi tsokacin ya nuna bakin cikinsa kan rikicin inda ya ce sanadiyyar daukan fansa ne da wasu ‘yan Fulanin da ake zargi ne ya tada rikicin.

Ya kuma umurci jami’an tsaron jihar (‘yan sanda da sojoji) da su mai da hankali wajen ganin sun hana maimacin irin wanna rikici sannan su sa baza turakansu domin hana aukuwar irin haka.

Share.

game da Author