Buhari ya fatattaki Babachir da Ayo Oke

1

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya Kori sakataren gwamnatin Tarayya, Lawali David Babachir da shugaban hukumar NIA Ayo Oke.

An nada Boss Mustapha a matsayin sabon sakataren gwamnatin Tarayya.

Babachir-David-Lawal.

Idan ba a manta ba, Kwamitin sanata Shehu Sani ta kama Babachir da kamfanin sa da yin harkalla a kwangilar cire ciyawa a Kogi Yobe.

Ganin korafe-korafen da ake tayi akai ne shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada wata kwamiti na musamman domin gudanar da bincike akai inda bayan haka ta mika masa abin da ta bankado.

Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci Kwamitin.

Share.

game da Author