Buhari ya ci gaba da Zama Ministan Mai ko ya nada wani? Abin da yan Najeriya suka ce

0

‘Yan Najeriya da dama sun tofa albarkacin bakinsu game da rikicin Ministan Mai Ibe Kachikwu da Shugaban kamfanin mai na kasa Maikanti Baru.

Wasu da yawa na ganin ci gaba da zama a kurarar babban ministan mai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya akai yanzu na daga cikin dalilan da ya sa shugabannin biyu suka kasa jituwa a tsakaninsu.

Mutane sama da 50 da muka tattauna da su a musamman jihohin arewacin Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu akan wannan badakala.

Wasu daga cikin wadanda suka tattauna da gidan jaridar PREMIUM TIMES HAUSA sun fito karara sun nuna rashin amincewarsu da ci gaba da zaman Buhari babban ministan mai na kasa.

Abubakar Hamza, ya ce ” Idan har ana so a sami yadda ake so toh dole ne a nada sabon babban minista da zai dinga lura da ayyukan ma’aikatan mai na kasa abar Buhari ya fuskanci jagoranci da yake yi wa kasa.”

” Ni a gani na aikin zai yi masa yawa kuma da yawa daga cikinsu suna amfani da hakan wajen yin wasu abubuwan da ba haka ba.”

Malama Halima Mohammed, Ta ce ba dole bane sai Buhari ya ci gaba da zama minista ba. ” Da dai zai nada wani ya rike kujerar ministan shi kuma ya mai da hankali wajen rike kasa kawai da yafi.”

Asabe Hassan ta ce ita bata ga wani abin cecekuce game da kujeran ministan mai da shugaban Kasa ya ke rike da shi ba. ” Abin da ake so shine a sami daidaituwa da nasara a aiki kuma ana samu saboda haka babu laifi don ya rike kujeran ministan mai na kasa din.”

Tijjani Bala kuwa cewa yayi da za abi nashi da ba ma za ayi ministan mai ba gaba daya. ” Tun da kowani ma’aikatan mai na da shugaba da ke kula da ita. Shugaban kamfanin mai na kasa zai iya rike ma’aikatan mai din. Ya na kai rahoto wa shugaban kasa akai akai.

Akalla kashi 75 na wadanda suka tofa albarkacin bakin su sun ce da dai Buhari zai nada wani da yafi.

Share.

game da Author