Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin a gaggauta koran Abdulrasheed Maina daga aiki sannan shugaban maikata na kasa Oyo-Ita ta gaggauta mika wa ofishin shugaban Kasa bayanan yadda akayi Abdulrasheed ya koma aiki ta bayan fage.
Hukumar EFCC na neman Maina ruwa a jallo saboda hannu da aka samu yana dashi wajen batan biliyoyin kudaden fansho a lokacin yana shugabantan hukumar.
Femi Adeshina ne ya sanya wa wannan takarda hannu.