Buhari bai sanar mana ko zai sake tsayawa takara ba, saboda haka kowa na iya takara a jam’iyyar – Bisi Akande

0

Tsohon shugaban jam’iyyar APC Bisi Akande ya ce har yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari bai sanarwa ‘ya’yan jam’iyyar ko zai nemi takarar shugabancin kasa ba. Saboda haka ko wanene ma ya ke so ya nemi kujerar zai iya fitowa domin fafatawa a zaben dan takara.

Bisi ya ce idan har akayi wannan zaben ko waye ya zama dan takara zasu mara masa baya a jam’iyyar.

Bayan haka kuma sun jinjina wa gwamnonin da jami’an gwamnati da suka fito daga yankin Kudu Maso Yamma kan ayyukan da suke yi cewa suna kokari sosai kan abin da suke yi wa kasa.

Share.

game da Author