Boko Haram sun maida yara 53, 311 marayu a Barno – Gwamna Shettima

0

Gwamna Kashim Shettima na Barno ya bayyana cewa kungiyar Boko Haram sun maida yara 52,311 marayu a yankin Arewa maso Gabas.

Shettima ya yi wannan jawabin ne yau a Maiduguri yayin da ya ke rattaba yarjejeniyar aikin Fadama III tsakanin jihar sa da Bankin Duniya.

Ya kara da cewa mata kimanin 54,911 suka rasa mazajensu sanadiyyar rikicin Boko Haram. Inda ya kara da cewa akasarin wadanda Boko Haram suka fi tagayyarawa mata ne da kananan yara.

“Idan muka kasa wajen kulawa da wadannan mata da kananan yara nan da shekaru 10 zuwa 15, idan mu ka kasa samar musu muhalli, to na tabbata su ma nan gaba ba za su jikan mu ba.”

“Kuma babu wata kulawar da ta wuce bayar da ilimi, wadda ba mu da wani zabin da ya wuce yin hakan.”

Shettima ya kara da cewa gwamnatin jihar sa da Majalisar Dinkin Duniya da sauran wasu kungiyoyi su na kan kokarin su na samar da kayan agaji domin magance rikicin da ta’addanci ya haifar wa yankin.

Ana kuma kan gina asibitoci da makarantu a yankunan da aka ceto.

“Nan da ‘yan watanni masu zuwa za a daina jin mummunan labarin Boko Haram, za a samu zaman lafiya mai dorewa.”

Ya ce aikin habbaka noman damina da na rani duk ya na kankama. Ya na da yakinin cewa nasarar da sojoji su ka samu za ta kara samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Share.

game da Author